DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Wajibi a sauya yadda ake juya jam’iyyun siyasa a Nijeriya – Abbas Tajudden

-

Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Tajudeen Abbas, ya bukaci a inganta tsarin jam’iyyu a Najeriya domin su daina zama tamkar kamfanonin kasuwanci da shugabanninsu ke amfani da su don ribar kansu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN yace taron bitar wanda ya gudana a Abuja kan kudirin dokar gyaran jam’iyyu, Cibiyar bada taimakon Zabe ta Turai (ECES) ce ta shirya tare da hadin gwiwar YIAGA Africa da Cibiyar Kukah, Abbas – wanda Hon. Ishaya Lalu ya wakilta – ya ce dole ne a kara kaimi wajen sanya jam’iyyu su rika aiki da tsari da manufa.

Google search engine

Ya ce, duk da cewa Najeriya na bin tsarin mulkin shugabanci irin na Amurka, akwai tazara mai girman gaske wajen yadda ake rajista da kaka-gida da masu kudi kanyi wajen zuba jari a harkokin jam’iyyu.

Kakakin majalisar ya nuna damuwa da yadda yawancin jam’iyyun Najeriya ke fama da rashin tsari da akida, wanda hakan ke haddasa sauya sheka da karancin amincewar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tankiya tsakanin Nijer da Benin ta sa kasashen rufe ofisoshin jakadancin juna

Kasashen Benin da Niger sun kori jami’an diflomasiyyar juna a wani mataki na ramuwar gayya, bayan shafe kusan shekara biyu ana takun-saka a tsakaninsu, a...

‘Yan bindiga sun yi ajalin mutane fiye da 30 a jihar Neja

Aƙalla mutane 30, ciki har da mata, sun rasu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari Kasuwan Daji da ke ƙauyen Demo, Borgu LGA a...

Mafi Shahara