DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

-

Wadanda abin ya shafa sun yi aiki ne a lokuta daban-daban tsakanin shekarar 2014 zuwa 2024 a lokacin mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, amma ba su samu hakkokinsu ba tsawon lokaci.

A cewar mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Ibrahim Adam, an tsara raba kudaden ne a matakai uku daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025, inda ya ce matakin wani bangare ne na sake farfado da mutuncin wadanda suka taba hidimtawa al’umma a jihar.

Google search engine

Tsofaffin jami’an kananan hukumomi da abin ya shafa sun nuna godiya da jin daɗi game da wannan mataki, suna mai cewa hakan ya tabbatar da adalci da kishin jama’a daga bangaren gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Wannan mataki na daga cikin manufofin da gwamnatin ta Kano tace tana dauka gyaran kura-kuran da ta gada daga mulkin baya da kuma kafa sabuwar hanyar da ke cike da gaskiya, adalci da mutunta na kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

’Yan majalisar wakilai bakwai daga Akwa Ibom sun sauya sheka zuwa APC

Ana cigaba da samun rahotannin sauyin sheka a majalisar wakilai, yayin da ’yan majalisa bakwai daga Jihar Akwa Ibom suka koma jam’iyyar APC. Wadanda suka...

Jam’iyyar Labour tsagin Julius Abure ta ba Peter Obi sa’o’i 48 ya fice daga jam’iyyar saboda shiga hadakar ADC

Jam’iyyar Labour karkashin jagorancin Julius Abure ta bai wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, wa’adin sa’o’i 48 da ya fice daga jam’iyyar, bisa...

Mafi Shahara