DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Albashin N70,000 ba ya iya daukar nauyin ma’aikaci – Wasu ma’aikatan gwamnatin Nijeriya

-

Ma’aikatan gwamnati a jihohi daban-daban sun bayyana cewa sabon mafi karancin albashi na N70,000 ba ya isar karamin ma’aikaci musamman duba da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Wannan na zuwa ne a yayin da kungiyoyin kwadago ke bikin ranar ma’aikata ta bana a fadin Nijeriya.

Google search engine

A shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan Najeriya, hakama wasu jihohin sun amince da biyan ma’aikatansu fiye da N70,000.

Duk da haka, wasu ma’aikata a jihohi daban-daban sun nuna damuwarsu kan yadda albashinsu ke kasawa wajen biyan bukatunsu.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara