DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar wakilan Nijeriya ta ba gwamnonin Benue da Zamfara da shugabannin majalisunsu su wa’adin mako daya su gaggauta bayyana a gaban kwamitinta

-

Majalisar wakilan Nijeriya ta ba gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, da na jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da shugabannin majalisun dokokin jihunsu wa’adin mako guda domin su bayyana a gaban kwamitin majalisar kan korafe-korafen da jama’a a kansu.

Wannan umarni ya biyo bayan gaza halartar zaman sauraron koke-koke da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata a zauren majalisar da ke Abuja, duk da gayyatar da aka riga aka aikewa Gwamnonin.

Google search engine

Wannan korafi dai ya samo asali ne daga wani kudiri da Mataimakin Kakakin Yada Labarai na Majalisar Wakilai, Hon. Philip Agbese, ya gabatar a gaban zauren majalisar a ranar 27 ga Maris.

A zaman farko na kwamitin da aka gudanar ranar Alhamis, Hon. Douglas Akya daga mazabar Makurdi ta Kudu ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar da aka dakatar daga Jihar Benue, yayin da Hon. Aliyu Ango Kagara daga Talata Mafara ta kudu tare da Shugaban ‘Yan adawa na Majalisar Zamfara suka wakilci ‘yan uwansu da abin ya shafa.

Kwamitin ya jaddada muhimmancin bayyanar dukkan wadanda aka gayyata, tare da bayyana cewa rashin halarta na gaba na iya fassaruwa a matsayin raini ga majalisar da kuma shari’ar da ke gaban ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar Dattawan Nijeriya za ta tantance sabbin Hafsoshin tsaro da shugaba Tinubu ya nada

Majalisar Dattawan Nijeriya ta shirya fara tantance sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada, domin tabbatar da su. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill...

Ciyo bashi bayan cire tallafin man fetur ba dai-dai bane – Sarki Muhammadu Sanusi II

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya soki gwamnati bisa ci gaba da ciyo bashi duk da...

Mafi Shahara