Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, kan tsare tsohon dan majalisar wakilai Muhammad Gudaji Kazaure.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X jigo a jam’iyyar PDP ya bayyana tsare Kazaure a matsayin rashin bin doka da oda ne, ta hanyar kamawa da tsare ‘yan kasa ba tare da bin ka’ida ba.
Ya ba da misali da batun VeryDarkMan, wanda ya ce an sake shi ne bayan da jama’a suka nuna rashin jin dadinsu akan kama shi.
Atiku ya ce tun bayan kama tsohon dan majalisar a Kano aka garzaya da shi Abuja, har yanzu ba a gabatar da wata tuhuma ko yi wa iyalansa da lauyoyinsa da kuma al’ummar Najeriya karin bayani.