Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya sanar a shafinsa na X cewa, kasashen sun amince da Shirin tsagaita wuta cikin gaggawa.
Shugaba Trump ya sanar da cewa Amurka ta shiga Tsakani wajen sulhunta abokan hamayyar da kowanne ke da makamin nukiliya.
A ‘yan kwakin nan kasashen biyu sun yi musayar makamai masu linzami da Kuma hare-haren bama-bamai da suka hada da tura jirage marasa matuka da harsasai.