Rukunin farko na maniyyata 420 daga jihar Kebbi sun tashi daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello International Airport da ke Birnin Kebbi, zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya.
Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris, tare da Amirul Hajj na Kebbi Kuma Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera da Shugaban Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kebbi, Faruq Aliyu Yaro Enabo su ne suka yi wa maniyyatan bankwana.
A jawabansu daban-daban, sun yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa goyon bayan da ya bayar, wajen tabbatar da fara jigilar alhazai cikin sauki.
Amirul Hajj ya tabbatar da cewa an kamala dukkan shirye-shiryen jigilar maniyyatan Kebbi 3,800 da suka hada da ba da fasfo, biza, ga maniyyata daga kananan hukumomi 21 na jihar.