Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuYan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina.

Jami’an sun yi artabu da ‘yan bindigar da ke dauke da muggan makamai, lamarin da ya tilasta musu tserewa da raunukan harbin bindiga.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Lahadi, ta ce jami’an sun yi nasarar dakile yunkurin dauke mutane goma da direbobi biyu da fasinjoji takwas – ba tare da sun ji rauni ba kuma suka koma ga iyalansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata