Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamna Zulum na Borno ya haramta sayar da fetur a yankin karamar...

Gwamna Zulum na Borno ya haramta sayar da fetur a yankin karamar hukumar Bama ta jihar

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya haramta sayar da mai a gidajen mai a karamar hukumar Bama da Banki.

Karamar hukumar Bama na a yankin arewa maso gabashin jihar Borno, kuma tana da iyaka da kasar Chadi sannan tana da iyaka da kasar Kamaru.

Umurnin ya biyo bayan tattaunawa tare da tuntubar hukumomin tsaro a jihar, da nufin magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce matakin na daga cikin dabarun da gwamnati ta dauka na dakile ayyukan tada kayar baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata