Sojojin Nijeriya sun yi nasara akan ‘yan bindiga 21 a dajin Shawu, dake Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr Nasiru Mu’azu Danmusa ya fitar a ranar Asabar dinnan.
A cewar sanarwar, dakarun runduna ta 17, sun kai wani hari a wani yanki da ‘yan ta’addan suke a karamar hukumar ta Faskari.
Farmakin ya yi sanadin halaka ‘yan ta’adda da dama da suka hada da wadanda ruwa ya tafi da su a lokacin da suke kokarin tserewa.
Kazalika an kwato babura kusan 40 da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba daga hannun ‘yan bindigar.
