Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuTinubu bai da niyyar dawo da tallafin man Fetur ko tsohon tsarin...

Tinubu bai da niyyar dawo da tallafin man Fetur ko tsohon tsarin musayar Kudi – Bayo Onanuga

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya bayyana cewa gwamnati ba za ta sauya matsayinta kan cire tallafin mai da hada darajar naira ba, domin ceto tattalin arziki.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya ce cire tallafi ya kawo karshen dogaro da NNPC kadai da kuma karancin mai, yayin da hada darajar naira ya dakile cin moriyar ‘yan tsiraru masu sayar da dala a kasuwar bayan fage.

Onanuga ya amince cewa akwai tsadar rayuwa, amma gwamnati ta dauki matakai don rage radadi, ciki har da dokar ta-baci kan abinci da saukaka shigo da magunguna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata