Sunday, April 5, 2026
HomeWasanniHar yanzu ba mu samu dala $100,000 da gidajen da Tinubu ya...

Har yanzu ba mu samu dala $100,000 da gidajen da Tinubu ya yi mana alkawari ba – Ajibade

Kyaftin din kungiyar Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya har yanzu ba ta cika alkawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa tawagar ba, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin zakarun Afrika na 2025 WAFCON da aka yi a Maroko.

A wata hira da ta yi da jaridar Guardian, Ajibade ta tabbatar cewa ba su samu dala $100,000 ba kuma ba a mika musu sauran kyaututtukan da aka yi alkawari ba, ciki har da gidaje.

Sai dai ta ce duk da haka, ’yan wasan na da kyakkyawan fata cewa gwamnati za ta aiwatar da alkawarin da ta dauka musu.

Ajibade wacce aka zaba a matsayin ‘yar wasan da ta fi kowa kwazo, ta jagoranci kungiyar zuwa lashe kofin WAFCON karo na goma wanda babu irinsa a tarihi a nahiyar.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata