DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba na jayayya da Shugaba Tinubu, kira kawai nake da a kara yin tuntuba kan dokar haraji – Gwamna Zulum

-

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira da a kara duba na tsanaki kan kudirin sake fasalin haraji da majalisar dokokin Najeriya ke nazari a kai, inda ya ce ba ya adawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. 
Zulum ya bayyana haka ne ta cikin wani shirin siyasa na gidan Talabijin na Channels, inda ya jaddada muhimmancin hada hannu da masu ruwa da tsaki don magance dukkan matsalolin da ke tattare da kudirin. 
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Dauda Iliya, ya fitar a Litinin din nan, Gwamna Zulum ya ce “tuntuba, babbar jigo ce ga al’ummar da ta rungumi tafarkin dimokuradiyya.”
Gwamnan ya nuna damuwarsa, tare da yin gargadin cewa wannan kuduri zai amfanar da jihohi kamar Lagos da Rivers ne kawai, abin da zai iya jefa sauran jihohin cikin mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Idan rikicin PDP ya ki ci, ya ki cinyewa za mu shiga kawance in ji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa dole na iya sanyawa jam’iyyar ta shiga kawance da wasu jam’iyyu idan ƙoƙarin da ake...

‘Yan sandan Nijeriya sun sanar da dawo da aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta sake fara aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu (Tinted Glass Permit), duk da...

Mafi Shahara