DCL Hausa Radio
Kaitsaye

NSA Ribadu ya gana da tawagar Majalisar Dokokin Amurka a Abuja

-

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya karɓi wata tawagar ‘yan majalisar dokokin Amurka a Abuja, domin ci gaba da tattaunawa kan al’amuran tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin sakon da ya wallafa a X, Ribadu ya ce ziyarar ta biyo bayan ganawarsu ta baya a Washington D.C., wadda ta mayar da hankali kan manyan batutuwan haɗin gwiwar tsaro.

Google search engine

Tawagar ta ƙunshi ‘yan majalisa kamar Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore, tare da halartar jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills. Ribadu ya ce hakan na nuna muhimmancin da ƙasashen biyu ke bai wa haɗin gwiwar tsaro.

A cewar NSA ɗin, tattaunawar ta ta fi karkata kan yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zaman lafiya a yankin, da hanyoyin inganta alaƙar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Ziyarar ta zo ne a lokacin da ake takaddama kan batutuwan diflomasiyya, musamman bayan matakin gwamnatin Amurka na mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take ’yancin addini, matakin da Najeriya ta musanta.

A baya-bayan nan, Ribadu ya gana da Sakataren Yaƙin Amurka Pete Hegseth, sannan Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa US–Nigeria Joint Working Group domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

IHR ta bukaci a mayar da rarar kudaden da Alhazan 2025 suka biya

Wata kungiyar fararen hula wadda ke gudanar da harkokin da suka shafi addini mai suna 'Independent Hajj Reporters' ta sake mika kira ga hukumar kula...

‘Yan sanda sun koka da yawan yada labaran karya a Nijeriya – IGP

Shugaban 'yan sanda a Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce babu wata hukuma a Najeriya da ke fuskantar mummunan tasiri daga labaran karya kamar ‘yan...

Mafi Shahara