DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta ki amincewa hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello ba tare da lauyansa ba

-

Kotun tarayya dake Abuja ta dage sauraren karar da hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta shigar akan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello har sai ranar 13 ga watan Disamba 2024.
Mai Shari’a Emeka Nwite ta dage zaman ne bayan da a farko ta dage sauraren karar har sai 21 ga watan Janairu 2025.
Sai dai lokacin da aka tambayi Yahaya Bello lauyansa, ya shaidawa an sanar da shi zaman kotun ne cikin dare hakan ya sa bai samu damar kiran lauyoyinsa ba.
Sai dai alkalin kotu ya umurci EFCC ta ci gaba da tsare shi kuma ta sanar da lauyoyinsa ranar 13 ga watan Disamba da kotun za ta sake zama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara