Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin Nijeriya za ta dawo da harajin saukar jiragen 'Helicopter' na $300...

Gwamnatin Nijeriya za ta dawo da harajin saukar jiragen ‘Helicopter’ na $300 a filayen jiragen kasar

Hukumar kula da iyakokin sama na Nijeriya ta ce za ta soma karɓar harajin saukar jiragen ‘Helicopter’ na dala 300 a filayen jiragen kasar nan ba da jimawa ba.
Wannan na zuwa ne watanni shida da gwamnatin tarayya ta dakatar da harajin saboda kin amincewar kamfunnan jiragen sama.
Da yake jawabi a wurin babban taron kungiyar ma’aikatan jiragen sama, darakta mai kula da sufurin jiragen sama na hukumar Mista Tayo John, ya ce ta hanyar karɓar haraji za su magance kalubalen kudaden da suke fuskanta.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata