Fadar shugaban kasa ta ce yunkurin juyin mulkin da aka dakile a Jamhuriyar Benin ya kara nuna rawar jagoranci da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke takawa wajen kare dimokuraɗiyya da zaman lafiya a Yammacin Afirka.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar Lahadi wasu sojoji karkashin Lt. Col. Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na gwamnati a Cotonou, inda suka yi ikirarin hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon.
Sai dai dakarun gwmnatin kasar da ke tsaron fadar shugaban kasar sun sanar da tarwatsa su cikin gaggawa.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban Nijeriya kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun, ya fitar a shafinsa na X, ya ce martanin Nijeriya cikin sauri ya tabbatar da matsayin Tinubu na kare tsarin mulki a yankin.
