Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock a ranar Juma’a, karo na farko tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau mulki, abin da ya ja hankalin jama’a ganin yadda ya dade bai halarci fadar ba.
Obasanjo, wanda ya sha sukar gwamnatin Tinubu, ya halarci taron Service of Nine Lessons and Carols na 2025 da Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya.
A taron, ya tuna da lokutan da Nijeriya ke da cikakken tasiri a Afirka, inda ya ce tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter kan sanar da Nijeriya duk wani mataki da Amurka za ta dauka a Afirka.
Kodayake bai yi tsokaci kai tsaye kan rikicin kalaman Amurka da Nijeriya ba, kasancewar Obasanjo a Aso Rock tare da manyan baki irinsu Janar Yakubu Gowon ya kara ɗaga darajar taron, tare da sake bude tattaunawa kan matsayar Nijeriya a idon duniya.



