DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-baci

-

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da ikon Shugaban Kasa na ayyana dokar ta-baci a kowace jiha domin hana tabarbarewar doka da oda.

A hukuncin da ya samu rinjayen kaso 6–1, kotun ta ce shugaban kasa na da ikon dakatar da zababbun shugabanni a lokacin dokar ta-baci, amma dole ne hakan ya kasance na dan wani lokaci ne kawai.

Google search engine

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Mai shari’a Mohammed Idris ya ce Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki ya ba shugaban kasa damar daukar matakai na musamman domin dawo da zaman lafiya, kodayake bai fayyace irin matakan ba.

Hukuncin ya shafi karar da Jihar Adamawa da wasu jihohin PDP 10 suka shigar, suna kalubalantar dokar ta-baci da Shugaba Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers, inda aka dakatar da gwamna da sauran zababbun jami’ai na tsawon watanni shida, inda Kotun ta yi watsi da karar.

Sai dai Mai shari’a Obande Ogbuinya na da sabanin ra’ayi, yana cewa ko da shugaban kasa na iya ayyana dokar ta-baci, ba shi da ikon dakatar da zababbun shugabanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Trump ya shigar da kara kan BBC, yana neman diyyar dala bilyan 5

Shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da kara a kotu yana neman diyya ta dala bilyan 5 (kimanin fam biliyan 3.7) kan BBC, bisa zargin...

Marigayi Buhari ya nuna cewa mulki amana ce, ba hanyar tara dukiya ba – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana marigayi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin jagora mai karfin hali cikin natsuwa da kan ladabi, kuma mai...

Mafi Shahara