DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedAn kori kungiyar Lakurawa daga Nijeriya - Sanata Aleiro

An kori kungiyar Lakurawa daga Nijeriya – Sanata Aleiro

Sanata Adamu Aleiro mai wakiltar Kebbi ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce sojojin Nijeriya sun kori sabuwar kungiyar nan ta Lakurawa zuwa Jamhuriyar Nijar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau jumu’a, Sanatan ya ce wannan nasarar ta samu ne bayan da ministan tsaro Abubakar Badaru, da babban hafsan soji da sauran hukumomin tsaro su kaddamar wa Lakurawa.
A cewarsa, tun ranar 12 ga watan Nuwamba da sojoji suka isa yankin Sokoto da Kebbi su ke fatattakar yan bindigar, kamar yadda jaridar Dailytrust.
Aliero ya ce tuni da sojoji suka gargada yan ta’addar suka bar iyakar Nijeriya, inda ya ce yanzu ya ragewa sojojin Nijar su gama da su saboda na kasar ba zasu iya shiga Jamhuriyar Nijar domin yaki da su ne ba.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata