Babbar Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta amince da belin tsohon ministan shari’ar Nijeriya Abubakar Malami, SAN, wanda ke fuskantar zarge-zargen cin hanci daga hukumar EFCC.
Umurnin kotun ya fito ne a ranar 23 ga Disamba, 2025, inda mai shari’a Justice Bello Kawu ya yanke hukuncin amincewa da belin Malami bayan sauraron roƙon gaggawa (motion ex-parte) da lauyansa ya shigar, tare da la’akari da hujjar da aka gabatar a gaban kotu.
Kotun ta umurci Malami da ya miƙa fasfo dinsa na ƙasashen waje, tare da cika sharuddan beli kamar yadda EFCC ta tanada tun da farko. Daga cikin sharuddan akwai bayar da masu tsayawa masa mutum biyu, ciki har da Darakta Janar na wata hukumar shari’a da kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Augie/Argungu.
Har ila yau, kotun ta amince da sake farfaɗo da sharuddan belin da aka cika a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga Janairu, 2026.



