DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedTarin bashin da kake ciyowa ke jikkata tattalin arzikin Nijeriya, sakon Atiku...

Tarin bashin da kake ciyowa ke jikkata tattalin arzikin Nijeriya, sakon Atiku Abubakar ga Shugaba Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya ce tarin bashin da gwamnatin APC ke ciyowa na kassara tattalin arzikin kasar.

Atiku ya kuma zargi majalisar dokoki ta kasar da zama taimakawa wajen jefa kasar cikin bashi.

Da yake martani kan bashin da majalisar ta amince Tinubu ya ciyo na baya-bayannan, Atiku ya ambato wani rahoto na bankin duniya wanda ya ce ya dora Nijeriya a mataki na uku cikin kasashen da tulin bashi ya yi wa yawa.

Tsohon shugaban ya bayyana damuwa aka yadda gwamnatin ke ci gaba da cin bashi, duk da cewa a watan Yuli shugaba Tinubu ya ce hukumar tattara haraji ta kasa da hukumar kwastam sun samar da kudade ga kasar wadanda ba a taba gani ba.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata