Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen aiwatar da Dokar Haraji ta kasa daga 1 ga Janairu, 2026, duk da ce-ce-ku-cen da ke gudana kan zargin an yi sauye-sauye a cikin dokokin da aka wallafa.
Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Kudi da Sauye-sauyen Haraji, Mr Taiwo Oyedele, ya bayyana wannan matsaya bayan ya yi wa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu bayani a Legas.
Ya ce an tsara wadannan sauye-sauyen ne domin rage wa ‘yan Nijeriya radadi da nauyin rayuwa, ba wai don tara kudaden shiga cikin gaggawa ba.

Maqaryatan banza, Wallahi ni dai Kobo aka dauka a cikin Account nawa Allah ya isa ban yafe ba. Kuma da yardar Allah Gwamnatin APC Gwamnatin Azzalumai ta gama mulki, 2027 sai mun kayar daku Insha’allahu…