Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuEFCC ta yi watsi da zargin Gwamna Bala Mohammed na tsangwamar jami'an...

EFCC ta yi watsi da zargin Gwamna Bala Mohammed na tsangwamar jami’an gwamnatinsa

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati a Nijeriya ta yi watsi da ikirarin da Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Bauchi, ya yi na cewa ana amfani da hukumar wajen tsangwamar sa da jami’an gwamnatinsa ta fuskar siyasa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, EFCC ta bayyana zargin a matsayin “karya” tana jaddada cewa hukumar na gudanar da ayyukanta ne cikin ‘yanci ba tare da katsalandan na siyasa ba.

Hukumar na mayar da martani ne ga kalaman Gwamna Bala Mohammed, inda ya yi zargin cewa wasu masu ruwa da tsaki na siyasa na amfani da EFCC wajen muzanta shi da makusantansa, musamman Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya.

EFCC ta ce ayyukanta na bin doka da oda ne kawai, tare da tabbatar da cewa ba ta aiki bisa umarnin kowace jam’iyya ko mutum, illa bin ka’idojin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata