Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai yanke alaƙa da Nyesom Wike, Ministan Abuja, saboda rikicin siyasar da ke tsakanin Wike da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ba.
Fayose ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a Arise TV, yana mai cewa Wike ya fi Fubara muhimmanci ga gwamnatin Tinubu, duba da rawar da yake takawa a siyasa da kuma aikinsa a matsayin Ministan Abuja.
A cewarsa, Tinubu ba shi da wani dalili da zai sa ya bar Wike, wanda ya goyi bayan zabensa a Rivers kuma yake taka muhimmiyar rawa wajen ba da nasarori ga jam’iyyar APC.
Maganganun Fayose sun zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dokokin Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Fubara bisa zargin aikata manyan laifuka, ciki har da rusa majalisar, kashe kuɗi ba bisa ka’ida ba da kin amincewa da ikon majalisar kamar yadda kotu ta umarta.
Rikicin siyasar Rivers ya samo asali tun ƙarshen 2023 sakamakon takaddama tsakanin Wike da Fubara kan ikon jagorantar tsarin siyasar jihar da kuma ikon PDP a tsakaninsu.
