Monday, April 6, 2026
HomeUncategorized'Yan sanda a Kaduna sun kama wasu da ake zargi da satar...

‘Yan sanda a Kaduna sun kama wasu da ake zargi da satar karfe layin dogo

  

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin karfen layin dogo ne tare da kwato mayan karafa guda 40 da suka sata a ranar Asabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Kaduna.

Hassan ya bayyana cewa wani mutum mai suna Yusuf Dogo, daga kungiyar ‘yan banga a Gnami a karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna ne ya zo ofishin ‘yan sanda inda ya kawo rahoton cewa ya ga wasu da ake zargin suna lalata hanyar jirgin kasa a Gnami.  

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata