Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedAmurka ta kama wani shugaban karamar hukuma a Nijeriya kan zargin badakalar...

Amurka ta kama wani shugaban karamar hukuma a Nijeriya kan zargin badakalar $3.3m

 FBI ta Amurka ta kama wani shugaban karamar hukuma a Nijeriya kan zargin badakalar $3.3M

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) ta cafke zababben shugaban karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra, Franklin Ikechukwu Nwadialo, a lokacin da ya isa filin jirgin sama a jihar Texas ta Amurka.

An kama Nwadialo ne bisa tuhumar da ake yi masa kan zargin badakalar kudaden da suka kai kimanin dala miliyan $3.3m 

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar shari’a ta Amurka ta fitar, ta ce Nwadialo na fuskantar tuhume-tuhume 14 kuma zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 idan aka same shi da laifi.

Ana zargin Nwadialo da amfani da shafukan zamani irin su; Match da Zoosk da ke kulla soyayya ga yan mata da samari inda ya rika amfani da shi yana damfarar abokan soya

yyarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata