DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Jihar Kano ya roki kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar da su janye daga yajin aiki da suka tsunduma yi

-

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga kungiyar likitoci ta Nijeriya reshen jihar da ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi domin kaucewa jefa rayukan al’ummar Kano sama da miliyan 20 cikin hadari.

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya kafa wani kwamiti domin bincike kan zargin cin zarafin da kwamishiniyar jin kai ta jihar, Amina Abdullahi HOD,ta yi wa wata likita a ranar Litinin a asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano.

Kungiyar likitocin ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin awanni 48 da ta kori kwamishinan jin kai, kuma ta sha alwashin ci gaba da yajin aiki , idan har gwamnati ta gaza biya mata bukatar ta.

Sai dai gwamnan da ya ke mayar da martani kan lamarin a yayin wani taron manema labarai da akai kai tsaye a gidan gwamnatin jihar ya bayyana rashin jin dadin sa kan matakin da kungiyar ta dauka bayan wata rashin fahimta juna da aka samu tsakanin tsakanin su.

Gwamnan ya jaddada cewa kungiyar za ta iya baiwa kwamitin binciken damar gudanar da bincike kan lamarin tare da daukar kwakkwaran mataki, maimakon dai na ayyukan su hakan zai taba wa’yanda basu ji ba basu gani ba a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatocin Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta a Asabar dinnan

Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya sanar a shafinsa na X cewa, kasashen sun amince da Shirin tsagaita wuta cikin gaggawa. Shugaba Trump ya sanar...

Rukunin farko na Alhazan jihar Kebbi guda 420 sun tashi zuwa Madinah

Rukunin farko na maniyyata 420 daga jihar Kebbi sun tashi daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello International Airport da ke Birnin Kebbi, zuwa...

Mafi Shahara