Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedAn yi asarar sama da Naira biliyan 300 a yayin zanga-zangar da...

An yi asarar sama da Naira biliyan 300 a yayin zanga-zangar da aka yi a watan Agusta – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce an yi asarar sama da Naira biliyan 300 a zanga-zangar #EndBadGovernance da ta gudana a fadin kasar cikin watan Agusta.

Da yake jawabi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yayin da yake karbar yaran da aka kama yayin zanga-zangar bayan an sako su bisa umarnin shugaban kasa Bola Tinubu, Shettima ya ce an yi hasarar akasarin dukiyoyi da harkokin kasuwanci a yayin zanga-zangar.

 Ya ce duk da hujjojin da ake da su a kan yaran, shugaba Tinubu ya ba da umarnin a sake su ne saboda shi shugaba ne mai kula da bukatun al’umma.

                             

Shettima ya kuma yi kira ga gwamnoni da sauran jami’an gwamnati da su yi abinda ya kamata wajen sanya matasan masu amfani a cikin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata