Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa kwamitin wucin-gadi na mutum bakwai domin tattara da daidaita ra’ayoyin sanatoci kan kudirin gyaran Dokar Zaɓe, a yayin da ‘yan majalisa ke ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa tsarin zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da hakan bayan zaman sirri na tsawon awanni uku da aka yi a ranar Alhamis, inda ya ce kwamitin zai tattara ra’ayoyi tare da magance batutuwan da har yanzu ke buƙatar gyara a kudirin dokar.
Ya bayyana cewa Sanata Niyi Adegbonmire ne zai jagoranci kwamitin, tare da sanatoci irin su Adamu Aliero, Aminu Tambuwal, Adams Oshiomhole, Danjuma Goje, Tony Nwoye da Titus Zam.
Akpabio ya ce an bai wa kwamitin wa’adin kwanaki uku kacal domin kammala aikinsa tare da gabatar da rahoto ga majalisar nan da ranar Talata mai zuwa, yana mai jaddada cewa dole ne Majalisar Dattawa ta yi taka-tsantsan duk da cewa Majalisar Wakilai ta riga ta amince da kudirin.
A cewar kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin zaɓe, gyare-gyaren da ake shirin yi za su ƙarfafa sahihancin zaɓe, su ƙara gaskiya da kuma gina amincewar jama’a. Daga cikin muhimman sauye-sauyen akwai tsaurara hukunci kan sayen ƙuri’a, tura sakamakon zaɓe ta na’ura, tantance masu zaɓe ta hanyar lantarki, da kuma tabbatar da sahihancin zaɓe tun daga 2027.
