Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani wajen sasanta rikicin siyasa a jihar Rivers, inda suka gana da Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da Ministan Abuja Nyesom Wike, a fadar shugaban kasa, a daren Litinin.
Jaridar The Nation, ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin jihar Rivers ciki har da Wike da Fubara, tare da wasu shugabannin siyasa daga jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa Fubara ya yi alkawarin nuna girmamawa ga Wike a nan gaba, alamar cewa rikicin siyasa tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar na iya samun sassauci.
