Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuMun saurari kiran da aka ba da umarnin kama ni bayan wani...

Mun saurari kiran da aka ba da umarnin kama ni bayan wani ya yi kutsen wayar Ribadu – El-Rufai

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ya saurari wata tattaunawar waya da ya danganta da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, inda ya yi zargin cewa an bayar da umarnin kama shi.

Rahotanni sun ce jami’an DSS sun yi ƙoƙarin kama shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan dawowarsa daga Masar.

A wata hira da BBC Hausa, El-Rufai ya ce gwagwarmayar siyasa domin sauya gwamnati ta fara, yana mai cewa da tuni an gurfanar da shi idan akwai hujjar zargi a kansa.

A wata hira da ARISE Television, ya ce ba EFCC ba ce ke da hannu a lamarin, sai dai ya zargi ICPC da neman taimakon DSS domin kama shi, yana mai cewa lauyoyinsa sun riga sun tuntubi EFCC kan batun gayyata.

El-Rufai ya amince cewa sauraren kiran waya ba bisa ka’ida ba ne, amma ya dage kan cewa ya samu bayanan ne ta wata hanya. Har zuwa hada wannan rahoto, hukumomin da aka ambata ba su yi martani ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata