Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuNijeriya na da damar jagorantar Afirka ta zama babbar nahiya a duniya...

Nijeriya na da damar jagorantar Afirka ta zama babbar nahiya a duniya – António Guterres

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bukaci Nijeriya ta jagoranci Afirka wajen neman sauyi a tsarin duniya, yana mai cewa ƙasar na da ƙarfin da zai kai nahiyar mataki babba.

Guterres ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, a gefen taron koli na 39 na Kungiyar Afrik da aka gudanar an Addis Ababa, Habasha. Ya ce yawan al’umma, dorewar dimokuraɗiyya da albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da Nijeriya ke da su sun ba ta dama ta zama jagora.

Ya kuma yaba wa sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rawar da ƙasar ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel da ECOWAS duk da ƙalubalen tsaro na cikin gida.

A nasa bangaren, Shettima ya jaddada aniyar Nijeriya na ci gaba da aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya tare da neman gyaran tsarinta domin bai wa Afirka wakilci mai ƙarfi, yana mai cewa Nijeriya ta cancanci kujera ta dindindin a Kwamitin Sulhu inda bangarorin biyu suka yi alƙawarin ƙara zurfafa haɗin gwiwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata