DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba gudu ba ja da baya za muyi zaben kananan hukumomi ranar Asabar-Abba Kabir Yusuf

-

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ba gudu ba ja da baya za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar Asabar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mika tutocin takara na jam’iyyar  NNPP ga ‘yan takarar shugabanin kananan hukumomin jihar 44 da kansiloli a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, ya ce da taron wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a ranar Alhamis ya samu halartar manya-manyan mabiya da magoya bayan jam’iyyar.

A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Simon Ameboda ta rushe shugabanni da mambobin hukumar zaben jihar KANSIEC tare da dakatar da gudanar da zaben har sai an gyara hukumar yadda ya kamata. 

Gwamnan, ya ce a halin yanzu jihar ba za ta bari wasu suzo su dagula zaman lafiyar da ‘yan kasa ke samu ba, ya kara da cewa gwamnatin jihar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar KANSIEC na da dukkan goyon bayan da tsarin mulki ya ba shi wajen gudanar da zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwamishinan Jigawa ya mayar da rarar Naira miliyan 301 daga kudaden da aka ware don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan...

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta karɓi wasikun kulla kawance daga sabbin jakadun ƙasashe 8

A ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025, fadar gwamatin ta Jamhuriyar Nijar ta karɓi sabbin jakadun daga jakadun ƙasashen duniya guda takwas. Inda shugaban mulkin sojin...

Mafi Shahara