Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da beli ga tsohon Ministan Shari’a na tarayya, Abubakar Malami, da matarsa Asabe Bashir, tare da ɗansu Abdulaziz Malami.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayar da belin kan Naira miliyan 200 ga kowanne daga cikinsu tare da mutane biyu da za su tsaya musu.
Kotun ta kuma shar’anta cewa ɗaya daga cikin waɗanda za su tsaya musu dole ne ya ajiye takardun mallakar gida a unguwannin Maitama ko Asokoro, waɗanda ke cikin manyan unguwannin birnin Abuja.
Har ila yau kotun ta umarci waɗanda ake tuhuma da su miƙa fasfo dinsu na ƙasashen waje ga kotu.
Sai dai kotun ta ce har sai sun cika dukkan sharuddan belin, za su ci gaba da kasancewa a hannun hukumar kula da gidajen gyaran hali.
