Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedNada ni Minista ina cikin shirin hidimta wa kasa bai saba...

Nada ni Minista ina cikin shirin hidimta wa kasa bai saba wa doka ba – Hannatu Musawa

Hannatu Musawa

Ministar Al’adu, Hannatu Musa Musawa  ta bayyana cewa bata aikata wani abu da ya saba wa doka ba ta hanyar karɓar nadin minista yayin da take gudanar da wajibcin shekara ɗaya na yi wa kasa hidima wato  (NYSC).

Hakan ya biyo bayan ganowar da Ƙungiyar rubuce rubuce kan dokokin kare hakkin Dan Adam (HURIWA) tayi na  cewa Musawa tana yiwa ƙasa hidima a wani wuri a  Abuja.

A wancan lokacin, Emeka Megwa, Daraktan yada laabarai da hulɗa da Jama’a na NYSC, ya bayyana cewa rike matsayin minista yayin gudanar da hidimar ƙasa yana nufin keta dokar hukumar kula da masu yi wa kasa hidima

A wata tattaunawa da Daily Trust, Megwa ya bayyana cewa  duk wani ɗan bautar ƙasa da ya karɓi kowanne naɗin mukami na  gwamnati kafin kamalla hidimar kasa ya sabawa dokar hukumar kula da masu yi wa  kasa hidima ta NYSC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata