- Bankin Duniya ya amince da bayar da bashin dala miliyan 500 ta karkashin shirin International Development Association domin farfado da bangaren noma a Nijeriya, musamman ga kananan manoma da kuma inganta tsaron abinci.
Kudin za su tallafa wa shirin Nigeria Sustainable Agricultural Value Chains for Growth Project (AGROW), wanda ke da burin kara yawan amfanin gona, hada manoma da kasuwanni, da kuma samar da ayyukan yi a fadin kasar.
A cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar, ya bayyana cewa an amince da bashin ne a ranar 30 ga Maris, 2026, domin inganta aikin kananan manoma, karfafa darajar noma, da kuma bunkasa wadatar abinci da abinci mai gina jiki.
Bankin ya kuma jaddada cewa noma shi ne babban bangaren da ke daukar ma’aikata a Nijeriya, amma har yanzu yana fuskantar kalubale kamar karancin kayan aiki masu inganci, sauyin yanayi, da kuma rashin isasshen hanyoyin kai kayayyaki kasuwa.
Haka kuma, ya ce da dama daga cikin kananan manoma na rayuwa ne a matakin noma don ciyar da kansu kawai, yayin da matsalar rashin wadataccen abinci da ingantaccen abinci ke ci gaba da damun al’umma a fadin kasar.
