Hukumar zaɓen Nijeriya, INEC ta umurci dukkan kwamishinonin zaɓe na jihohi da su dakatar da duk wani shiri da ya shafi aikin sabunta katin zaɓe da aka tsara gudanarwa a faɗin ƙasar.
Jaridar The Guardian ta rawaito cewa wannan umarni na kunshe ne a cikin wata takarda da sakatariyar hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, inda aka buƙaci a dakatar da dukkan shirye-shirye da wayar da kan jama’a kan aikin har sai an bayar da sabon umarni.
Tun da farko, hukumar ta sanar da cewa za a fara aikin ne daga ranar 13 ga Afrilu, 2026, domin sabunta rijistar masu kaɗa ƙuri’a kafin zaɓen 2027.
