DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kanawa sun yi watsi da sabuwar zanga-zanga da aka fara a Nijeriya

-

 Mazauna Kano sun yi watsi da sabuwar zanga-zangar da aka fara a wasu sassan kasar, yayin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.

Google search engine

An fara yada zanga-zangar ranar 1 ga Oktoba, 2024, mai taken “FearlessInOctober”, a shafukan sada zumunta, wasu watanni biyu bayan zanga-zangar #EndBadGovernance ta Agusta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Da ta ke lura da halin da ake ciki a Kano, Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin da aka ware ranar 1 ga watan Oktoba domin hutu, mutane da dama sun zabi zama a gida.

Duk da haka, wasu sun tafi don gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum.

Manyan tituna sun dan yi shiru babu cunkoson ababen hawa, yayin da aka bude shaguna da sauran kananan sana’o’i.

Binciken gaggawa da aka yi a manyan kasuwanni kamar Kwari, Sabon Gari, Singer da Kurmi ya nuna cewa galibin kasuwannin su ma a bude suke sai dai shaguna ‘yan kalilan da ke a rufe.

Bayanai dai sun ce an fara gudanar da zanga-zangar a biranen Legas

da Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC na duba buƙatun kungiyoyi 110 da ke neman rigista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa ta karɓi wasikun buƙatun rajistar sabbin jam’iyyu 110 daga kungiyoyi daban-daban har zuwa Litinin, 23 ga watan...

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam'iyyar na kasa Jam’iyyar PDP ta dawo da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na kasa bayan...

Mafi Shahara