Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuNijeriya ta ware naira biliyan 135 ga shari’o’in zaben 2027

Nijeriya ta ware naira biliyan 135 ga shari’o’in zaben 2027

Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ware naira biliyan 135.22 a cikin kasafin kuɗin 2026 domin shari’o’i da al’amuran da ke biyo bayan zaɓen 2027.

Rahoton kasafin ya nuna cewa an sanya wannan kuɗi ne ƙarƙashin Service-Wide Votes, wato asusun da gwamnati ke amfani da shi wajen biyan kuɗaɗe da ba su da alaƙa da wata hukuma guda.

Bincike ya nuna cewa wannan tanadi na nufin gwamnati na sa ran yawaitar ƙorafe-ƙorafe da shari’o’i bayan zaɓe.

An kuma ware sama da naira tiriliyan 1 ga Hukumar zaben domin shirya zaɓen 2027, wanda ya kai kaso mai tsoka daga cikin kuɗaɗen da ake bai wa hukumomi kai tsaye.

Haka kuma, jaridar Punch ta ruwaito jimillar kuɗaɗen da aka ware ƙarƙashin Consolidated Revenue Fund sun kai naira tiriliyan 3.7, inda wannan sashe na shari’o’in zaɓe kaɗai ya kai kusan kashi 3.65 cikin ɗari.

Sai dai jam’iyyun adawa kamar PDP da ADC sun nuna damuwa kan wannan tanadi, suna cewa yana nuna cewa ana tsammanin zaɓen ba zai kasance mai karɓuwa ba.

Sun kuma buƙaci a ƙara nuna gaskiya a tsarin zaɓe, suna masu cewa idan aka gudanar da sahihin zaɓe, za a rage yawan shari’o’in da ke biyo baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata