DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta umurci hukumar EFCC ta tsare tsohon Gwamna Darius Ishaku

-

Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta sa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku da tsohon babban sakataren ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu Bello Yero a gidan yari bisa zargin laifukan cin hanci da rashawa.
An kama mutanen biyu ne a ranar 27 ga watan Satumba, bisa zargin karkatar da kudi N27bn mallakar ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu.
Sai dai, bayan gurfanar da su gaban kotu, wadanda ake tuhumar, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, ta ce ba su amsa laifin da hukumar ke tuhumarsu ba kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyarsa ta Al Nassr har zuwa shekarar 2027

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya a hukumance, inda zai ci gaba da zama a birnin Riyardh na kasar...

Mataimakin shugaban Nijeriya Kasshim Shettima ya tafi kasar Ethiopia

A safiyar ranar Alhamis Kasshim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birnin Adis Ababa domin ziyarar aiki bisa gayyatar da Firaministan kasar Dr Abiy Ahmed...

Mafi Shahara