Shugaban Amurka, Donald Trump, ya jawo Nijeriya cikin takaddama da kafar yaɗa labarai ta CNN kan wani rahoto da ya shafi matsayin Iran bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.
Rigimar ta ɓarke ne bayan Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka da Iran domin buɗe ƙofar tattaunawa.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin Truth Social, Trump ya musanta wani bayani da CNN ta watsa wanda aka danganta da hukumomin Iran, inda aka ce Tehran ta samu gagarumar nasara a rikicin.
Ya zargi CNN da cewa ta ɗauko rahoton ne daga wani shafin “labaran ƙarya” da ya ce yana da alaƙa da Nigeria, sannan ta gabatar da shi a matsayin sahihin labari.
Shugaban ya ƙara da cewa rahoton da aka watsa bai wakilci matsayar hukuma ta Iran ba, yana mai cewa sahihin bayani ya wallafa shi ne a shafinsa.
A wani ƙarin saƙo, Donald Trump ya zargi CNN da wallafa “ƙarya mai haɗari” wadda za ta iya ƙara rura wutar rikici a wannan lokaci mai sarkakiya, tare da kiran kafar da ta janye rahoton tare da ba da haƙuri.
Gidan talabijin na TVC News ya ruwaito rahoton da ake takaddama a kai, wanda aka danganta da Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce Tehran ta yi wa Amurka mummunar kaye tare da tilasta mata amincewa da wasu sharuɗɗan tattaunawa.
Sai dai Donald Trump ya ƙaryata hakan, yana mai cewa bayanin hukuma daga Iran bai nuna hakan ba.
A nata ɓangaren, CNN ta tsaya kan rahoton da ta wallafa, inda ta ce ta samo bayanan ne kai tsaye daga jami’an Iran tare da tabbatar da su daga kafofin yaɗa labarai na ƙasar.
Wani mai magana da yawun CNN ya ce sun bi ƙa’idojin aikin jarida wajen tantance sahihancin bayanan kafin wallafawa.
Lamarin ya ja hankali a Nigeria bayan zargin Trump, duk da cewa bai gabatar da wata hujja ba kan cewa rahoton ya samo asali daga wani shafin Najeriya.
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Tarayyar Amurka, Brendan Carr, ya mara wa Trump baya, inda ya soki yadda CNN ta gudanar da rahoton, yana mai kiran a ɗauki mataki kan abin da ya kira labarin ƙarya.
Wannan na zuwa ne yayin da duniya ke ci gaba da mayar da martani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, wadda ake kallon ta a matsayin wata hanya ta rage tashin hankali, duk da cewa kowanne ɓangare na ikirarin samun nasara a rikicin.
