Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kuɗin Nijeriya Tanimu Yakubu, ya bayyana cewa kasar ba ta cikin hadarin rushewar tattalin arziki, saboda yanzu haka ana aikin Tukur domin garambawul ga tsoffin manufofin tattalin arziki.
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Yakubu ya amince cewa jama’a na fuskantar matsi, amma hakan wani ɓangare ne na gyare-gyaren da gwamnati ke aiwatarwa.
Ya ce, duk da halin ƙunci da ake ciki, bai kamata a ɗauke shi a matsayin rushewar tsarin tattalin arziki ba, domin ƙasashen da tattalin arzikinsu ya rushe ba sa iya aiwatar da manyan gyare-gyare kamar daidaita farashin canjin kuɗi, ƙara kudaden ajiya na ketare, da kuma samun damar shiga kasuwannin kuɗi na duniya.
Jaridar The Nation ta ruwaito Yakubu ya ƙara da cewa a baya tsarin tattalin arzikin ƙasar ya kasance kamar mai ƙarfi, amma a zahiri cike yake da matsaloli kamar tallafin man fetur, tsarin canjin kuɗi da kuma kashe kuɗin gwamnati ba tare da wani sakamako ba.
A cewarsa, cire waɗannan tsare-tsare ya haifar da tsadar rayuwa a yanzu, amma ya ƙara gaskiya da inganta yadda ake tafiyar da tattalin arziki.
Dangane da kuɗaɗen shiga na gwamnati, ya ce an samu ƙaruwar fiye da kashi 40 bisa ɗari bayan cire tallafin man fetur, yayin da bashin ƙasar ke ƙasa da kashi 30 cikin ɗari na kudin shiga, kuma ajiyar kuɗaɗen waje sun haura dala biliyan 40, kamar yadda bayanan babban bankin kasar suka nuna.
