Thursday, April 9, 2026
HomeBabban LabarinmuAmurka ta fara janye ma’aikatan ofishin jakadancinta daga Nijeriya 

Amurka ta fara janye ma’aikatan ofishin jakadancinta daga Nijeriya 

Gwamnatin Amurka ta fara janye wasu ma’aikatan ofishin jakadancinta da iyalansu daga Abuja, sakamakon karuwar matsalolin tsaro a Najeriya.

A cikin sabon gargadin tafiya da ta fitar, Amurka ta bukaci ‘yan kasarta da su sake tunanin tafiya zuwa Najeriya, tana mai bayyana damuwa kan yawaitar laifuffuka, ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma rikice-rikicen cikin gida.

Gargadin ya ce manyan laifuffukan tashin hankali irin su fashi da makami, kwacen mota da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sun zama ruwan dare a sassa daban-daban na kasar.

DW Africa ta ruwaito, Amurka ta ce ‘yan kasarta za su iya fuskantar hari, kasancewar ana kallonsu a matsayin masu arziki.

Bugu da kari, ta yi gargadin cewa barazanar hare-haren ta’addanci na nan daram, musamman a wuraren taruwar jama’a kamar kasuwanni, manyan shaguna, otel-otel, wuraren ibada da kuma wuraren taruka.

Rahoton ya kuma nuna cewa bangaren kiwon lafiya a Najeriya na da karancin inganci da kuma rashin daidaito, inda yawancin cibiyoyi ba su kai matakin da ake da shi a Amurka da Turai ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata