Thursday, April 9, 2026
HomeKasuwanciNijeriya ta fara hako gangar danyen mai miliyan 1.84 a rana -NNPCL

Nijeriya ta fara hako gangar danyen mai miliyan 1.84 a rana -NNPCL

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPCL ya bayyana cewa yawan ɗanyen mai da Najeriya ke samarwa ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.84 a rana a matsayin mafi girma, sakamakon inganta tsaron bututun mai.

Shugaban kamfanin, Bashir Bayo Ojulari, ne ya bayyana haka a wani taron majalisa kan tsaron bututun mai da aka gudanar a Abuja.

Ya ce samar da mai ya tashi daga ganga dubu 960,000 a rana a shekarar 2022 zuwa ganga miliyan 1.71 a rana, tare da kaiwa ganga miliyan 1.84 a shekarar 2025.

Ojulari ya danganta wannan nasara da sabon tsarin tsaron makamashi da aka kafa a yankin Niger Delta, wanda ya haɗa da haɗin gwiwar gwamnati, hukumomi, kamfanoni da kuma al’ummar yankin.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ya ce rage satar mai da lalata bututun mai ya taimaka wajen dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari a fannin mai da iskar gas.

A nasa jawabin, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin ƙara bunƙasa samar da mai.

Haka kuma, majalisar wakilai ta buƙaci a ci gaba da duba yadda ake tafiyar da tsarin domin tabbatar da adalci da daidaito.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da na tsaro, ciki har da shugabannin hukumomin tsaro da masu kula da harkokin mai na kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata