Ministan tsaro na Najeriya, Christopher Musa, ya umarci hukumomin tsaro da na leƙen asiri su daina aiki a rarrabe, tare da ƙarfafa haɗa bayanan sirri domin inganta tsaro a ƙasar.
Jaridar Punch ta ambato shi ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya yi da jami’an harkokin leƙen asiri a Abuja.
Ya ce samun ingantattun bayanan sirri na da matuƙar muhimmanci wajen tallafa wa dakaru, musamman a yaƙin da ke bukatar amfani da fasaha, inda barazana ke fitowa daga ciki da wajen ƙasa.
Ministan ya ce duk da cewa hukumomin tsaro na kokari, amma rashin haɗin kai yana rage tasirin ayyukansu.
Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin dukkan rundunoni da hukumomi domin inganta tsaro.
Haka kuma, ya buƙaci ‘yan ƙasa su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da inganta ayyukan dakarun.
Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro irin su ta’addanci, garkuwa da mutane da ‘yan bindiga, lamarin da ya sa ake ƙara jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.
