Mataimakin Shugaban Kasa Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron majalisar dinkin duniya karo na 79
Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na wannan shekara ba.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar.
Sanarwa tace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa halartar taron.
Shugaba Tinubu, wanda ya dawo Nijeriya a Lahadin da ta gabata bayan tafiyar zuwa kasashen China da Birtaniya, yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida da kuma magance wasu matsalolin da kasar ke fuskanta, musamman bayan da aka yi fama da ambaliyar ruwa a fadin kasar.
A yayin taron majalisar dinkin duniya na 79, mataimakin shugaban kasa Shettima zai gabatar da jawabi ga mahalarta taron, tare da halartar muhimman wurare, da kuma gudanar da taruka a tsakanin kasashen biyu.

