Jam’iyyar APC a jihar Bauchi ta bayyana cewa a shirye take ta karɓi gwamnan jihar, Bala Abdulkadir Mohammed, yayin da yake shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.
Wannan na ƙunshe ne cikin bayanin da mambobin kwamitin APC na jihar Bauchi suka fitar bayan wata ganawa da suka yi da gwamnan a gidansa da ke Abuja, inda suka tattauna kan shirin sauya sheƙarsa zuwa APC.
Sakataren kwamitin APC na jihar kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Toro, Dabo Isma’il, ya bayyana cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan yadda gwamnan zai shiga jam’iyyar cikin lumana.
