DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeSiyasaBabu wani abin tayar da hankali a Nijeriya - Gwamnatin Tinubu

Babu wani abin tayar da hankali a Nijeriya – Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa ‘yan ƙasar da kuma ƙasashen duniya cewa har yanzu ƙasar na cikin aminci, duk da matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na janye ma’aikatan ofishin jakadancinta da iyalansu daga Abuja.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce gwamnati na sane da damuwar da aka nuna, amma ya jaddada cewa Nijeriya na ci gaba da kasancewa ƙasa mai tsaro ga mazauna da baƙi masu zuwa.

Tun da farko, Amurka ta ba da umarnin ficewar ma’aikatanta marasa muhimmanci daga ofishin jakadancinta da ke Abuja, tare da dakatar da hidimar bayar da biza a can, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin tabarbarewar tsaro a wasu sassan ƙasar.

Sai dai ofishin jakadancin Amurka da ke Lagos ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukansa, ciki har da bayar da biza.

Jaridar Punch ta ambato jihohin da aka ware sun haɗa da Borno, Yobe, Kogi, Kwara, Niger, Filato, Taraba, Jigawa da arewacin Adamawa, tare da wasu jihohi kamar Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara.

Haka kuma a Kudanci da Kudu maso Gabas, an shawarci ‘yan Amurka da su guji zuwa jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da Rivers (ban da Fatakwal).

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa duk da waɗannan gargadi, hukumomin tsaro na aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya, tare da roƙon jama’a su kwantar da hankalinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata