Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya fitaccen ɗan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote, murnar zagayowar ranar haihuwarsa a Juma’ar nan, 10 ga Afrilu, 2026.
A cikin saƙon da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya yaba da irin gudunmawar da Dangote ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya da ma nahiyar Afirka.
Ya ce hangen nesa, jajircewa da ƙirƙira na Dangote sun taimaka wajen gina manyan masana’antu, ciki har da matatar mai ta Dangote Refinery da kuma kamfanonin siminti a faɗin Afirka.
Shugaban ya kuma yabawa rawar da kamfanonin Dangote ke takawa wajen samar da ayyukan yi da gina ababen more rayuwa, tare da jaddada cewa hakan na nuna cikakken amincewarsa da tattalin arzikin Nijeriya.
Haka zalika, ya jinjinawa ayyukan jin ƙai da ake gudanarwa ta hannun Gidauniyar Dangote Foundation, musamman a fannonin lafiya, ilimi da rage talauci.
A ƙarshe, Bola Ahmed Tinubu ya yi addu’ar Allah ya ƙara wa Aliko Dangote lafiya, hikima da ƙarin nasarori domin ci gaba da hidima ga Nijeriya da duniya baki ɗaya.
